Kanwan Katsina SHUGABA ABIN KOYI By Kabir A. S/Kuka
Masu iya magana na cewa, itaciya mai zaki tun daga furenta ake ganewa. Wannan batu haka yake, domin duk É—an kwarai yana fitowa ne daga gidan kwarai. Daga cikin irin su har ila yau akan samu shuwagabanni na kwarai wanda duk irin yadda suka kai kololuwa a fannin mulkin su, to basu watsi da na kasan su. Hasalima, kullum kokarin janyo su a jika suke yi.
Alhaji Usman Bello Kankara mni na daga cikin irin wadannan shugabanni da kowane lokaci suke zama abin koyi kuma abin bayar da misali ta irin yadda suke tafiyar da rayuwar su acikin al'umma.
HAZIKI MAI BASIRA
Idan zamu tuno wasu abubuwan da Kanwan na Katsina Alhaji Usman Bello Kankara mni yayi tun a lokacin yarintar shi, a makarantar Boko da Islamiya sai da ya zamo abin nan da ake cewa, Gagarabadau, domin tarihi ya nuna, babu wani darasin da za'a koyar ba tare da ya fahimce shi kuma ya hardace shi tamkar kai kace shi ne mai koyarwa. Wannan lamarin ya bashi damar yin karance-karancen shi har ya gama ba tare da ya fuskanci wata matsala ba.
Kafin shigar shi aikin gwamnati, Alhaji Usman Bello ya fara da yin aikin jarida bayan ya gama aikin yiwa kasa hidima NYSC a inda ya fara da gidan rediyon tarayya dake Kaduna. Wannan aikin jarida da fara ya ba shi damar karar sanin yadda zai tafiyar da al'umma baya ga wancan na bautar kasa da yayi a jahar Bendal, watau can kudancin kasar, inda za'a iya cewa babu wani dsn-uwa dake wajen, amma saboda iya tafiyar da jama'a yasa har inda ya zauna suka yi bikin karrama shi bayan nuna alhinin rabuwa da shi.
Ba ina wannan rubutu tare da kawo wasu shekaru na wasu abubuwan da Kanwan yayi ba, a'a, manufar rubutun koyon darasin shugabanci daga irin rayuwar da shi Alhajin yayi ce a baya da kuma halin da ake ciki a yanzu. UK. Bello kamar yadda wasu ke kiran shi, bai jima da yin aikin jarida ba ya samu aiki a hukumar hana fasa kwabri ta kasa(Nigeria Customs Service). To dama masu iya magana na cewa, wani ma yayi rawa bare dan makadi? Wato, É—an da ya fito a gidan mulki ya saba ganin shigi da ficin da ya kama tun daga jama'a har ya kai ga kaya ko dukiya da sauran su, ba sai ance ba, tun daga gida ya fara koyon sanin makamar aiki.
A HUKUMANCE
Tun daga ranar da Alhaji Bello Kankara ya fara aiki, tun daga wannan lokaci abubuwa suka ci gaba da wakana na dangantaka tsakanin da jama'a. Akwai wasu muhimman abubuwan da har gobe hukumar Kwastan ba zata manta da shi ba akan su, kai hatta da kasar baki daya ana cigaba da amfana da wancan aiki na basira da yayi ba. Batun samun kudin shiga daga wannan hukuma, Alhajin ya bayar da gudunmuwa ta kirkiro da wata hanyar samun kudin shiga musamman daga can ɓangaren yankin tafkin Chadi inda ake hada-hadar kifi musamman busasshe. Ma'aikacin ya fahimci irin asarar da gwamnatin Najeriya ke yi ta wannan fuska ta shigi da fici a tsakanin kasashen. Bada bata wani lokaci ba, ya bullo da hanyar kaɓar haraji daga masu sana'ar. Ai kafin kace kwabo, sai ga wasu sabbin kudin shigar na shigowa a lalitar hukumar. Wannan abu ba karamin kwarjini ya karawa jami'in ba, abin da ba'a san da shi ba ana ta asara amma shi cikin ɗan lokaci ya kawo hanya mafita a matsayin shi na jagora a wajen.
Wannan lamari yasa likkafar jami'in ta cigaba da yin sama. Anan fa banyi maganar wadanda suka samu ɗaukaka ta hanyar shi ba walau ta fuskar aiki ko harkokin kasuwanci da sauran irin su ba, nan gaba za'aji. Al'amura sun cigaba da kankama har ya zamo duk inda wani sashe na hukumar ya samu rauni, to za'a tura Agogo sarkin aiki domin daidaita lamurra. Hakan yasa har ya kai ga rike matsayin babban Kakakin (PRO) hukumar na kasa. Matsayin da ya rike kuma yayi amfani da shi wajen fadakar da jama'a irin aikace-aikacen hukumar da wasu ke yiwa kallon hadarin kaji saboda rashin sanin muhimmancinta. A lokacin UK Bello 'yan kasuwa masu shiga kasashen waje suka gane cewa, ashe suna da muhimmanci a wajen tayar da komaɗar tattalin arzikin kasa, ashe a wasu lokuttan suna kashe kansu ne suna raya wasu? Ma'ana, suna biyan haraji a wasu kasashen suna habaka su yayin da nan gida suna aiwatar da akasin haka. Har'ila yau, a lokacin yana Kakakin ne jama'a suka ƙara bambance kayan da ake fadan shigowa ko fita da su, sannan suka san yaya ma zasu rika saduwa da jami'an hukumar na asali don yin hudatayya domin an rika samun bata gari.
Kafin in tsaya a wannan rubutu nawa kashi na farko, zan ɗanyi tsokaci akan yadda har Allah ya bashi sarautar gida wadda ya gaji mahaifin shi marigayi Kanwan Katsina Alhaji Bello(Allah ya gafarta mashi) sarautar da marigayi Sarkin Katsina Alhaji Muhammadu Kabir Usman(Allah ya gafarta mashi) yayi mashi kuma a lokacin Alhaji Usman yana cikin aikin shi. Dama ita wannan sarauta ta Kanwa ta mayaƙi ce jajirtacce wanda yake zama gagarabadau a fagen daga. Hawan mukamin Alhaji Usman Bello bisa wannan kujera ta hakimcin Ƙetare ya kara mashi wani ƙwarin gwiwa tare kuma da cigaba da bijiro da irin ilhamomin da Allah yayi mashi ta fannin shugabanci ga al'ummar shi.
Allah Kara lafiya da Nisan kwana ga Mai Girma Kanwan Katsina Hakimin Ketare Alhaji Usman Bello Masari mni
ReplyDelete