ƘASAR FARANSA CE KE ƊAUKAR NAUYIN TA'ADDANCIN DA AKE YI A AFIRKA - Firaministan Mali
Daga Kabir Ahmed S/Kuka
A zauren majalisar ɗinkin duniya, firaministan rikon kwarya na kasar Mali ya furta zafafan kalamai ga kasar Faransa da abokanta
A ranar karshe na babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 77, Abdoulaye Maiga ya zargi masu hannu cikin matsalar tsaro da ta addabi kasar Mali da sauran ƙasashen Afirka. Da farko, ya tunatar da Antonio Guterres, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya cewa, ya sani shi ba "shugaban kasa ba ne". Haka ma shugaban kasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embaló, wanda ke shugabantar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS cewa, maganarsa bata dace da matsayin sa ba. Shi ma shugaban Nijar, Mohamed Bazoum, bai kyale shi ba, firaministan Mali ya bayyana shi a matsayin "baƙon da ke ikirarin cewa shi dan Nijar ne al'hali ba haka ba ne". A karshe wacce ta fi shan suka, kasar Faransa ce, inda ya ce ita"take tallafawa da kuma ba da makamai ga 'yan ta'addan da suke yakan su, kuma ya ce yana da hujjojin tabbatar da hakan.
Maganganun Firaministan Na ƙasar Mali a yayin taron Na Majalisar Dinkin Duniya,Na daga cikin Abubuwan da suka fi ɗaukar hankalin Jama'a a zauren taron.