Aikin Hajj 2022 : HAJJ REPORTERS TA KARRAMA GWAMNA MASARI

Aikin Hajj 2022: HAJJ REPORTERS TA KARRAMA GWAMNA MASARI 

Daga Abdulhadi Bawa SSA, Abuja

Aikin Hajji yana daga cikin shika-shikan Musulunci, hakan yasa gwamnatoci suke bashi muhimmanci tare da daukar matakan saukaka ma Mahajjata yadda za su gudanar da aikin.
Independent Hajj Reporters, kungiya ce mai zaman kanta, ta fitattun 'yan jarida masu lura da yadda ake tafiyar da hidimar Mahajjata a kasa mai tsarki tare da hada rahotanni a kan aikin Hajji da kuma Umra domin amfanin gwamnatoci, hukumomi, kungiyoyi da kuma al'umma. A cikin wannan aiki nata ne, wannan kungiya ta gano cewa gwamnatin jihar Katsina, a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta yi zara kuma da dara sa'o'inta wajen kula da kuma kyauta jin dadin Alhazai a kasa mai tsarki, kama tun daga shekarar 2015 har zuwa 2022.
A yau, a babban dakin taro na babban Masallacin kasa (National Mosque) dake Abuja, Independent Hajj Reporters ta karrama Gwamna Aminu Bello Masari a matsayin Gwamnan da yafi kyautatawa tare da kula da jin dadi da walwalar Mahajjata.

Post a Comment

Previous Post Next Post